FAQ

Yaya zan yi na dakatar da yawan email da Bakandamiya ke aiko min a kullum?

Mutum na iya dakatarwa ko tsagaita wayan email dake zuwa mi shi daga taskar Baakandamiya.

Da farko sai ka je profile na ka/ki ta hanyar latsa hotonka. Da zarar an je profile, za a ga abubuwa guda hudu, sai a latsa “Notifications”. Bayan an latsa za a ga an yi ticking (canki) duk email dake zuwa wa mutum. Sai a yi unticking wanda ba a so yake zuwa sannan a yi saving daga sama hannun dama.

Yaya zan yi tagging na mutum a Bakandamiya?

Da farko sai kai abokin mutum ne kafin ka iya tagging na shi. Kuna iya binciko yadda ake zama aboki, wato adding friend.

Bayan ka zama abokin mutum, a yayin da kake rubutu sai ka sanya alamar @ sannan ka biyo (kada ka sa space) da rubuta sunan mutumin da kake so ka yi tagging. Da zarar ka fara, sunayen abokanka za su fito a jere har da sunan mutumin, sai ka latsa kan sunanshi ka zaba. Sunan zai shigo inda kake rubutu. Shikenan sai ka ci gaba da rubutunka idan baka gama ba, ko kuma ka yi posting idan ka gama. Abokin naka zai samu sako, wato notification, cewa ka yi tagging na shi. Wannan zai sa ya shigo don duba abinda ya sa ka yi tagging na shi.