Yadda za a yi sign up a Bakandamiya ta browser
Sign up a Bakandamiya ta browser duk daya ne ko da mobile phone za a yi amfani ko kuma da computer. Amma a wannan screenshots na kasa mun yi amfani ne da mobile phone.
Da farko dai sai a nemi website na Bakandamiya ta browser; ta Chrome, Opera ko wata browser daban da kuke amfani da ita, irin su Vidmate da makamantan su.
A halin yanzu babu Bakandamiya a Playstore.
Idan aka bude browser sai a sanya www.bakandamiya.com a yi browsing, zai bude shafin farko kamar yadda yake a wannan screenshot da ke kasa.
Idan mutum dama ya na na da account, kai tsaye sai ya sanya login details na shi (emil da kuma password), sannan ya latsa sign in ya shiga. Idan kuma sabon account za a bude, wanda shi ne makasudin wannan bayani, sai a latsa ‘Join.’
1. Join
Da zarar an latsa ‘join,’ to za a je shafi na gaba inda za a sanya email da kuma password da kuma wasu sauran bayanai.
2. Email Address
3. Password
4. Password Again
Wajen password zaka ga an saka 6 characters, 1 uppercase, 1 lowercase, 1 number, 1 special.
- 6 characters na nufin kada ya gaza yawan kalmomi guda shidda misali: Habiba
- 1 uppercase na nufin akalla harafi guda daya mai babban baki misali: D
- 1 lowercase na nufin harafi guda daya mai karamin baki misali: d
- 1 number na nufin lamba guda daya misali: 5
- 1 special yana nufin special harafi guda daya, misalin special harafi ya hada da: /@$(?#
Misalin password zai iya zama: HabibaD5@
Kuma password sau biyu za a sa, shi ne ‘password again.’
Har ila yau, idan aka kula a yayin da kake rubuta password din za a ga cikin dan akwatin da aka rubuta uppercase da lowercase din yana cikewa, yana yin green din kala. Da zaran duka sun yi green, to ya nuna cewa password din ka ya samu karbuwa.
5. Username
Username must be alphanumeric. Hakan na nufin zaka hada sunanka da lamba, misali: Habiba5
6. Profile Type
A zabi irin kalar account da ake son budewa. Idan naka ne wanda za ka bude da sunanka, sai a zabi ‘Personal.’ Idan kuma don wata sana’a ce ko kungiya wanda kake son budewa da sunar sana’ar ko kungiyar, sai a zabi ‘Organization.’
7. Time Zone
A zabi time zone a nan. Idan ba ka san time zone na ka ba, to ka bar shi yanda ka gan shi.
8. Human Verification
A danna akwatin dake kasa da wannan don verification. Zai yi ticking.
9. I’ve read and agree to the terms of service
Sai a danna akwatin da ke jiki don amincewa da ka’idojin amfani da Taskar Bakandamiya.
Bayan an cike komai sai a danna ‘continue‘ in da zai je shafi na gaba.
10. Verification Code
Bakandamiya zata aiko da verification code (lambobi guda 6). Sai a sanya su, sanna a latsa ‘save.‘
Da zarar shafin verification code ya wuce babu wata matsala, to za a je shafin da za a cike bayanai da suka shafi suna, jinsi da makamantansu.
11. Sunan Farko
12. Sunan Karshe
13. Jinsi
14. Ranar Haihuwa
15. Takaitaccen Bayani
16. Sunan Gari
17. Karamar Hukuma
18. Sunan Jaha
19. Sunan Kasa
Bayan an cike bayanan baki daya, sai a latsa ‘save,’ inda zai kai ka zuwa shafin da za a sanya hoto kamar yadda yake a kasa.
20. Choose File
Nan waje ne da za a saka hoto ta hanyar dauko shi daga gallery din waya. Sai a danna hoton a zaba, zai maida ka site din kamar yadda yake a kasa nan.
Sai kuma a dannan ’save.’
Ana dannan ‘save,‘ zai kai mutum shafi na karshe. A nan a danna ‘SKIP THIS STEP’ kawai.
Shikenan an kammala bude account a website din Bakandamiya. Yanzu za a shigo shafin farko, wato activity feeds, kamar yadda yake a screnshot na kasa.
Da yawa zasu ce hanyar na da tsayi, wannan gaskiya ne. Bakandamiya website ne da ya yarda da saka matakan tsaro saboda masu kutse da ake kira da (hackers) a Turance don kare account na mambobinta.